Isa ga babban shafi
Habasha

Yunwa ta yi tsanani a Habasha

Fari na sake illa a Kasashe da dama na Afrika
Fari na sake illa a Kasashe da dama na Afrika Waldo Swiegers/Bloomberg via Getty Images

Hukumomin Habasha sun ce adadin ‘Yan kasar da ke bukatar taimakon abinci saboda matsalar fari ya karu zuwa sama da miliyan bakwai da rabi.

Talla

Hukumar ta ce tana bukatar tallafin abinci domin tallafawa wadanan mutane nan da karshen wannan shekara.

Hukumar agajin gaggawa a Habasha ce ta yi wannan kiran inda ta ce yanzu haka yankunan Oromia da Amhara da SNNP suna fama da tsananin karancin ruwan sha tare da kuma yankunan da aka samu fari.

Hukumar ta ce suna bukatar sama da ton 432,000 na abinci domin tallafawa mutane da ke matukar bukatar taimako .

Rahoton hukumar kiyaye bala’o’I a Habsha ta yi gargadin cewa karancin ruwan sama da ake hasashen za a iya samu a bana zai jefa mutane sama da miliyan 5 da rabi cikin matsanancin hali na bukatar abinci a yankunan Oromia da Amhara da kuma wasu yankunan kudancin kasar.

Hukumar ta kuma bayyana cewa suna bukatar kudi da ya kai kimanin Dala miliyan 742 domin tunkararar matsalar.

Matasalar fari bara ta shafi mutane sama da miliyan 10 a fadin Habasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.