Isa ga babban shafi
Nijar

Masu safarar ‘yan ci-rani sun zargi gwamnatin Nijar da saba alkawali

Ana safarar 'yan ci rani daga yankin Agadez na Nijar zuwa Libya zuwa Turai
Ana safarar 'yan ci rani daga yankin Agadez na Nijar zuwa Libya zuwa Turai AFP PHOTO / BOUREIMA HAMA

Kungiyoyin da ke sana’ar safarar ‘yan ci rani a a Jamhuriyyar Nijar ta hanyar Agadez zuwa Turai sun bayyana bacin ransu kan yadda  aka kasa mutunta alkawurkan da suka cim-ma da hukumomin kasar.

Talla

Kungiyoyin a baya sun amince ta dakatar da duk wata harka da ta shafi safarar bakin haure idan hukumomi sun dau musu alkawarin samar ma su da wani aiki na daban.

Acikin watan mayu shekarar 2015 gwamnati Nijar ta sanya hannu a kan wata doka da ke hukunta duk wani mutun da aka samu da laifin safarar bakin haure tare da alkawalin samar wa masu sana'ar da sabbin ayyukan yi

Oumar Sani ya aiko da rahoto daga Agadez.

Masu safarar ‘yan ci-rani sun zargi gwamnatin Nijar da saba alkawali

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.