Isa ga babban shafi
Nijar

Nijar: Ambaliya ta rusa gidaje sama da 400 a Abala

RFIHAUSA/Awwal

Ambaliya ta shafe gidaje sama da 400 a garin Abala cikin jihar Tileberi a Jamhuriyyar Nijar sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka tafka a yankin tsakanin jiya zuwa yau Laraba.

Talla

Rahotanni sun ce mutane da dama ne ke ficewa daga garin bayan rasa muhallinsu.

A garin Abala ne kwanan baya wasu ‘yan bindiga suka kai hari.

Duk shekara dai Nijar na fuskantar ambaliyar ruwa da ke shafar sassa da dama na kasar, kuma da ke haddasa barna ga gidaje da konaki tare da asarar rayuka.

Za ku iya kallon hotunan ambaliyar.

Ambaliya ta tafi da gidaje a Abala cikin Nijar

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.