Isa ga babban shafi
Gabon

Yan Sanda sun kama wani dan adawa a Gabon

Ali Bongo Shugaban kasar Gabon
Ali Bongo Shugaban kasar Gabon AFP/Steve Jordan

Yan Sanda a kasar Gabon sun capke wani dan adawa mai suna Roland Desire Aba’a Minko wani dan gaban goshi jigo yan adawa Jean Ping da ake zargi da tuzura jama’a dama yi barrazanar tada bama-bamai a wasu ofishoshin Gwamnati . 

Talla

Dan adawan ya furta wadanan kalamai ne a gaban mutun –mutunmi tsohon Shugaban kasar Leon Mba dake babban birnin kasar Libreville.

Wata majiya daga Libreville na nuni cewa wasu mutane dauke da makamai sun habkawa wasu gidajen rediyo na kasar inda suka bukaci ma’aikantan da su yadda wasu labarai na nuna kin goyan bayan ga Shugaban kasar Ali Bongo Ondimba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.