Isa ga babban shafi
Gabon

Kotun ICC ta gudanar da bincike a Gabon

'Yan adawa sun yi watsi da sakamakon zaben Gabon
'Yan adawa sun yi watsi da sakamakon zaben Gabon AFP PHOTO / XAVIER BOURGOIS

Jami’an kotun hukunta manyan laifufuka da kuma cin zarafin bil’adama ta duniya sun kammala aikin da ya kai su kasar Gabon wanda ya shafi binciken farko dangane yiyuwar aikata laifufuka bayan zaben da aka gudanar a kasar a bara.

Talla

A yanzu dai jami’an da suka gudanar da binciken za su mika rahotonsu ne ga alkalan kotun domin duba yiyuwar aikata laifufuka.

Jami’an sun gana da ministan tsaro da na cikin gida da na shara’a da na sadarwa da kuma jagoran ‘yan adawa Jean Ping.

Bangaren gwamnati da na ‘yan adawa na zargin juna da aikata laifufuka bayan zaben, wanda ‘yan adawa suka ki amincewa da sakamakonsa.

Rikici dai ya barke ne jin kadan bayan bayyana sakamakon zaben shugaban kasa inda aka bayyana shugaba Ali Bongo a matsayin wanda ya lashe zaben.

Dan takarar adawa Jean Ping ya yi watsi da sakamakon zaben wanda aka gudanar a watan Agustan bara tare da zargin an yi magudi musamman lura da yawan kuri’un da aka kada shi.

Rikicin ya janyo hasarar rayuka inda bangaren adawa suka ce sama da mutane 50 aka kashe, amma kuma alkalumman gwamnati suka ce mutum uku ne akwai suka mutu.

Tun Kafin isowar tawagar ta ICC yan adawa suka bukaci shugaba Ali Bongo ya yi murabus, tare yin da barazanar kona gine-ginen gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.