Isa ga babban shafi
Najeriya

NDLEA ta kama wata Mata da damen tabar wiwi a Lagos

An kama matar a Lagos
An kama matar a Lagos NDLEA

Hukumar da ke hana sha da fataucin Miyagun kwayoyi a Najeriya NDLEA, ta sanar da cafke wata mata da ton 7.5 na tabar wiwi a wani samame da ta kai yankin Badagary da ke Jihar Lagos a kudancin kasar.

Talla

Mataimakin Shugaban Hukumar ta Kasa, Sulaiman Ahmad Ningi, ya shaidawa Rfi hausa cewa sun gano matar ne bayan samun bayanai tana gudanar da sana’ar tabar a gidanta tare da mijinta a yankin na Badagary.

Mista Ningi ya ce Matar mai suna Timilehin Vincent Iyama kawai jami’ansu suka kama yayin da mijinta ya gudu.

Matar da mijinta sun dade suna sana’ar kuma Mista Ningi ya ce ton yakan kai sama da miliyan 30 na wiwi.

NDLEA za ta gabatar da matar a gaban kotu domin fuskantar shari’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.