Isa ga babban shafi
Faransa-Africa

Faransa na nazarin kafa sansanonin saukar Bakin-Haure

Kafa sansanoni saukar bakin hauren na da nufin bayar da tsaro ga lafiya da kuma dakile safarar su baya ga kaucewa hadarin da suke shiga a tekun Medtraniyam
Kafa sansanoni saukar bakin hauren na da nufin bayar da tsaro ga lafiya da kuma dakile safarar su baya ga kaucewa hadarin da suke shiga a tekun Medtraniyam REUTERS/Pascal Rossignol

Faransa na shirin gabatar da shawarwarin samar da Sansanonin bakin-Haure a kasashen jamhuriyar Nijar da Chadi a wani bangare na cimma alkawarin da shugaba Emmanuel Macron ya yi na ganin an samu raguwar asarar rayukan yan ciranin da ke haurawa kasashen Turai dama dakile matsalar safarar Mutane.

Talla

A cewar ministan harkokin wajen Faransa Mr Jean Le Drian, lokacin da ya ke mai da jawabi gaban majalisar dokokin kasar kan shirin shugaban na samar da sansanonin a kakar Bana, ya ce, yanzu haka suna nazarin inda ya dace su kafa sansaanonin tarben bakin hauren a kasashen jamhuriyar Niger da Chadi, domin samun damar shawo kan matsalar ta kwararar bakin hauren.

Yanzu haka dai mahukuntan Fransa na nazari ta kyakyawar huldar da ke tsakaninta da kasashen jamhuriyar Nijar da Tchadi, da hukumar kula da yan gudun hijira ta MDD da tuni keda irin wannan sansanin tarben bakin haure, tare da hadin guiwar hukumar shige da fice a duniya.

Mr Le Drian ya kara da cewa suna tattaunawa da aminansu kamar Italiya da sauran mambobin Kungiyar tarayyar turai domin cimma nasarar abinda suka sa gaba.

Me Le Drian ya ce babbar manufar gwamnati Faransa a kan wadannan sansanoni shi ne tabbatar da tsaron rayukan masu neman mafakar siyasa da kuma kaucewa mummunan halin da bakin haur ke jefa kansu a tekun Medtraniyam haka kuma tare da yakar masu safarar bakin hauren.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.