Isa ga babban shafi
Africa ta Kudu

Jam’iyyar ANC na zargi Khoza da haddasa rarrabuwar kai

Jacob Zuma, Shugaban kasar Afrika ta Kudu
Jacob Zuma, Shugaban kasar Afrika ta Kudu © REUTERS/Rogan Ward

Jam’iyyar ANC mai mulki a Africa ta Kudu, ta kori daya daga cikin jiga-jiganta, Makhoza Khoza, mutumen da ke shugabancin kwamitin majalisar kasar kan tafiyar da al’amuran yau da kullum, biyo bayan zazzafar adawar da ta ke cigaba da nunawa gwamnatin shugaban kasar Jacob Zuma.

Talla

Jam’iyyar ta ANC ta zargi Khoza da haddasa rarrabuwar kai tsakanin ‘ya’anta.

An dai fara zaman doya da manja tsakanin Khoza da shugabannin ANC bayanda a farkon watan da muke ciki ta fito karara ta bayana cewa zata kada kuri’ar rashin goyon bayan gwamnatin Zuma a zaben da majalisar kasar ta yi a sirrance a ranar 8 ga watan da muke ciki, kan goyon baya ko rashinsa ga gwamnatin mai ci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.