Isa ga babban shafi
Kamaru

Boko Haram ta kone kauyen Gakara a Kamaru

Yankin arewa mai nisa a Kamaru na ci gaba da fuskantar barazanar hare haren Boko Haram
Yankin arewa mai nisa a Kamaru na ci gaba da fuskantar barazanar hare haren Boko Haram AFP PHOTO / REINNIER KAZE

Rahotanni daga kamaru sun ce mayakan Boko Haram sun abka wani kauye a tsakiyar daren jiya a arewacin kasar inda suka cinna wuta tare da kashe mutane 15 da kuma sace wasu mutane 8.

Talla

Lamarin ya faru ne a kauyen Gakara yankin Kolofata da ke kusa da kan iyaka da Najeriya.

Rahotanni sun ce gidaje sama da 30 ne ‘yan Boko Haram suka cinnawa wuta.

Wata majiya ta ce mayakan sun harbe mutanen 15 ne har lahira tare da kone wani mutum guda da ransa.

Yankin Kolofata da ke yankin arewa mai nisa a Kamaru dai na ci gaba da fuskantar barazanar hare haren ‘yan Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.