Isa ga babban shafi
Najeriya

sama da mutane dubu dari ne ambaliyar ruwa ta shafa a Benue

Ambaliya a garin Abala na Nijar
Ambaliya a garin Abala na Nijar RFIHAUSA/Awwal

Sama da mutane dubu dari daya ne suka rasa muhallansu sakamakon ambaliyar ruwa a jihar Benue a Tarayyar Najeriya, sakamakon ruwan sama mai karfi da aka sama a yankin a cikin ‘yan kwanakin nan.

Talla

Mafi yawa daga cikin mutanen da ambaliyar ta shafa na zaune ne a birnin Makurdi fadar gwamnatin jihar ta Benue, yayin da jami’an hukumar agajin gaggawar ta kasar wato NEMA ta fara aikin isar da kayayyakin jinkai domin jama’a.

 

A shekarar ta bana dai an samu ambaliyar ruwa a jihohi da dama na yankin tsakiya da arewacin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.