Isa ga babban shafi
Najeriya-Kamaru

Amnesty ta shawarci Najeriya da Kamaru a kan Boko Haram

Shugaban mayakan Boko haram Abubakar Shekau tare da mayakansa
Shugaban mayakan Boko haram Abubakar Shekau tare da mayakansa News Ghana

Kungiyar Amnesty International tace sabbin hare haren da kungiyar Boko Haram ta kaddamar, daga watan Afrilu na wannan shekara, sun yi sanadiyyar mutuwar fararen hula 381 a kasashen Kamaru da Najeriya, yayinda wasu miliyoyi ke bukatar agajin gaggawa.

Talla

Amnesty tace alkaluman da ta tattara a Arewacin Kamaru da Jihohin Barno da Adamawa dake Najeriya na kunar bakin wake, na da tada hankali, ganin yadda kungiyar ke amfani da mata da kananan yara mata wajen kai hare-haren.

Yayin zantawar da yayi da sashin Hausa na RFI, Isa Sanusi, babban jami’in lura da sashin yada labaran kungiyar ta Amnesty International, ya ce kwai bukatar gwamnatocin Najeriya da Kamaru, su dauki matakan gaggawa domin kare fararen hula daga sabbin hare-haren.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.