Isa ga babban shafi
Gabon

Gwamnatin Gabon ta dagewa 'yan adawa haramcin tafiye-tafiye

Shugaban kasar Gabon Ali Bongo tare da mukarrabansa, yayin da suka kai ziyara fadar gwamnatin Faransa, a birnin Paris.
Shugaban kasar Gabon Ali Bongo tare da mukarrabansa, yayin da suka kai ziyara fadar gwamnatin Faransa, a birnin Paris. AFP PHOTO / ERIC FEFERBERG

Ma’aikatar harkokin cikin gida ta kasar Gabon, ta sanar da dage haramcin tafiye-tafiye zuwa kasashen waje, da ta kakabawa shugabannin ‘yan adawar kasar ciki harda abokin hamayar shugaba Ali Bongo wato Jean Ping.

Talla

A ranar lahadin makon da ya gabata ne, mai’aikatar cikin gidan Gabon ta haramtawa Jean Ping da mukarrabansa fita daga kasar, saboda kalaman da ya furta na neman tunzara ‘yan kasar su yi wa gwamnatin Ali Bongo bore.

Ma’aikatar ta ce ganin kalaman na Jean Ping bas u yi wani tasiri ba a tsawon mako guda, yasa ta dauki matakin dage takunkumin da ta kakaba masa.

A shekarar da ta gabata, Ping mai shekaru 74, ya sha kaye a zaben shugabancin kasar da ya fafata tsakaninsa da shugaba mai ci Ali Bongo, zaben da ya ce an tafka magudi a cikinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.