Isa ga babban shafi
Africa ta Kudu

Shugaba Jacob Zuma Ya Sake Fuskantar Matsalar Siyasa a Garin sa.

Shugaba Jacob Zuma na Africa ta Kudu.
Shugaba Jacob Zuma na Africa ta Kudu. rfi

Wata Kotu a kasar Africa ta Kudu ta zartas da cewa zaben da aka yi wa wani bangare dake goyon bayan Shugaba Jacob Zuma a kauyen sa shekaru biyu da suka gabata, ya sabawa doka saboda haka an soke.

Talla

Hukuncin Babban Kotun da aka zartas a Cape Town na nuna takun saka da ake samu cikin jam'iyar dake Mulki ANC, wanda zai iya dagula kokarin sa na ganin tsohuwar matarsa Nkosazana Dlamini-Zuma ta maye gulbinsa a matsayin shugaban kasa.

Yankin shugaba Jacob Zuma na KwaZulu Natal dake gabashin kasar na fama da rikici kuma yankin na da tasiri a wajen zabe a taron kasar na Babbar jam'iyar dake mulki ANC.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.