Isa ga babban shafi
Najeriya

Za a soma sharia'ar yan Boko Haram a Najeriya

'Yan kungiyar Boko Haram
'Yan kungiyar Boko Haram pmnewsnigeria

Gwamnatin Najeriya ta ce, nan da watan Oktoba mai zuwa za ta fara shari’ar mutane dubu 1 da 600 da ake zargin cewa mayakan Boko Haram ne.

Talla

Wata sanarwa da ma’aikatar shari’a ta kasar ta fitar ta ce, za a gaggauta gudanar da shari’ar bayan tsaikon da aka samu wajen gudanar da bincike kafin gurfanar da wadanda ake zargin.

Ministan shari’a Abubakar Malami ya ce, za a fara shari’ar a ranar 9 ga watan Oktoba, yayin da aka zabi kwararrun alkalai da za su jagoranci zaman shari’ar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.