Isa ga babban shafi
Kamaru

Kamaru: An dage bude jami'o'in yankin masu amfani da Ingilishi

Wani sashi na yankin Bamenda mai amfani da turancin Ingilishi a kasar Kamaru.
Wani sashi na yankin Bamenda mai amfani da turancin Ingilishi a kasar Kamaru. AFP/Reinnier KAZE

Hukumomin kasar Kamaru sun dakatar da shirin sake bude jami’oin kasar guda biyu dake Yankin masu amfani da turancin Ingilishi.

Talla

Wata sanarwar da fadar Firaminista ta fitar, ta ce, yayin da yau 26 ga Satumba ake shirin bude daukacin jami’oin gwamnati da masu zaman kan su, gwamnatin ta dage komawa karatu a jami’ar Buea da ta Bermenda.

Sanarwar ba tayi bayani ko jinkirta bude jami’oin na da nasaba da rikicin da aka samu a yankin ba.

A watan Oktoban bara ne dai mutanen yankin Baminda suka fara zanga zangar nuna adawa da yadda suka ce gwamnatin Kamaru na fifita yankunan da ke amfani da Faransanci a kansu, lamarin da ya nuna rabuwar kan da ke tsakanin yankunan kamaru biyu da kasashen Faransa da kuma Birtaniya sukai wa mulkin mallaka.

Akalla masu zanga zanga 6, jami’an tsaron kasar suka harbe yayinda suka kame wasu daruruwa, tun bayan fitowar dimbin jama’ar yankin don yin zanga zangar a wancan lokacin.

Bayan yakin duniya na daya, majalisar dinkin duniya ta mallakawa kasashen Faransa da Birtaniya yankunan kasar Kamaru, wadanda a baya suke karkashin kasar Jamus a dunkule.

Bayan samun ‘yancin kai a shekara ta 1960, mafi rinjayen al’ummar yankin da ke amfani da harshen turanci suka zabi kasancewa cikin Kamaru a maimakon Najeriya, sai dai kuma tun a waccan lokacin suka fara kokawa bisa cewar ana nuna musu wariya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.