Isa ga babban shafi
Afirka ta Kudu

Kotun Kolin Afrika ta kudu ta amince a binciki Zuma

Shugaban Afirka ta Kudu, Jacob Zuma.
Shugaban Afirka ta Kudu, Jacob Zuma. WU HONG / POOL / AFP

Sashen daukaka kara na Kotun Kolin kasar Afirka ta Kudu, ya bayar da umurnin fara bincike dangane da wasu zarge-zarge da ake yi wa shugaban kasar Jacob Zuma, kan cewa ya karbi rashawa a lokacin wani cinikin makamai da kasar ta yi a shekarun 1990.

Talla

Jacob Zuma da kansa ne ya shigar da kara a gaban kotun domin ta hana gudanar da bincike a game da wannan zargi da ake yi ma sa, inda kotun ta ce dole ne shugaban ya amsa tambayoyi a game da zarge-zargen rashawa har kusan 800 da ake yi masa.

Babban alkalin kotun Eric Leach, ya ce kasancewar Zuma shugaban kasa ba zai hana a binciki wannan zargi da ya samo asali a lokacin da yake rike da mukamin mataimakin shugaban kasar ta Afirka ta Kudu ba.

Bayanai na nuni da cewa Jacob Zuma, ya karbi milyoyin daloli shi da wasu manyan jami’an kasar ta Afirka ta Kudu, a lokacin da aka kulla wani cinikin sayen makamai akan dalar Amurka bilyan 5, inda kasar ta sayi manyan makamai ciki har da jiragen yaki daga wasu kamfanoni biyar na kasashen Turai.

A shekara ta 2005 ne kotu ta yanke wa wani na hannun daman Zuma mai suna Schahir Shaik hukuncin dauri shekaru 15 a gidan yari saboda samun sa da laifi a wannan batu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.