Isa ga babban shafi
Zimbabwe

ZANU-PF ta bai wa Mugabe wa'adin sauka daga mulki

Shugaban Zimbabwe Robert Mugabe yayin da ya halarci bikin yaye daliban jami'a a birnin Harare. 17 ga Nuwamba, 2017.
Shugaban Zimbabwe Robert Mugabe yayin da ya halarci bikin yaye daliban jami'a a birnin Harare. 17 ga Nuwamba, 2017. REUTERS/Philimon Bulawayo

Jam’iyya mai mulki a Zimbabwe, ZANU- PF ta kori shugaban kasar Robert Mugabe daga shugabancinta, zalika taron manyan wakilan jam'iyyar ya cimma matsayar hadawa da korar mai dakin shugaban kasar, wato dakinsa Grace Mugabe.

Talla

Manyan wakilan sun dauki matakin ne yayin wani taro da suka yi a tau Lahadi inda a yanzu suka zabi, tsohon mataimakin shugaban kasa, Emmerson Mnangagwa a matsayin sabon shugaban jam’iyyar ta ZANU-PF.

Zalika jam’iyyar ta zabi Mnangagwa a matsayin wanda zai yi mata takarar shugabancin kasar a shekara mai zuwa.

A halin da ake ciki ZANU-PF, ta debawa Robert Mugabe wa’adin awanni 24 da ya sauka daga shugabanci, ko kuma majalisar kasar ta tsige shi.

A ranar 6 ga watan Nuwamba, Mugabe ya kori, Emmerson Mnangagwa daga mukamin mataimakinsa, bisa zargin cewa yana kokarin kawo rarrabuwar kai a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar ta ZANU-PF, da kuma yunkurin cin amanar kasa.

Yayin wata zantawa da kamfanin dillancin labarai na AP, Chris Mutsvangwa, daya daga cikin tsaffin sojojin da suka kwaci 'yancin Zimbabwe daga mulkin mallaka, ya bayyana fargabar rikidewar zanga-zangar da wasu 'yan kasar ke yi na neman Mugabe ya yi murabus zuwa tashin hankali, muddin aka samu tsakon haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.