Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Mugabe ya ki amincewa da sauka daga Mulki

Shugaban Kasar Zimbabwe Robert Mugabe lokacin jawabinsa a daren jiya lahadi
Shugaban Kasar Zimbabwe Robert Mugabe lokacin jawabinsa a daren jiya lahadi STR / AFP

Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe na fuskantar barazanar tsigewa daga jam’iyyarsa ta ZANU-PF, bayan nuna turjiyar sanar da murabus kamar yadda jam’iyyar ta bukata.

Talla

A daren jiya Lahadi aka sa rai shugaban zai sanar da murabus a jawabin da ya gabatar ta kafar talabijin kasar, amma sai ya bige da jawabi kan batutuwan da suka shafi tattalin arziki da siyasa.

Kafin jawabin Mugabe mai shekaru 93 a duniya, wata Majiyar fadar shugabancin kasar, ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa, AFP cewa, Mugabe zai bayyana sauka daga shugabancin kasar, to amma sai aka samu akasain haka.

Har yanzu dai ZANU-PF na kan bakanta na wa’adin da ta bai wa Mugabe ya sauka daga mulki zuwa wannan ranar ta litinin kamar yadda jigo a jam’iyyar kuma tsohon kakinta Rugare Gumbo ke cewa yayin tattaunawar da RFI.

A jiya Lahadi Jam’iyyar mai mulki a Zimbabwe, ZANU- PF ta kori Robert Mugabe daga shugabancinta, tare da maye gurbinsa da mataimakinsa da ya kora Emmerson Mnangagwa.

Mugabe da ya soma Mulkin Zimbabwe a matsayin Friminista a shekara ta 1980 ya shafe sama da shekaru 30 yana karagar Mulki.

Zimbabwe a yanzu na cikin yanayin dari-dari abin da zai iya biyo bayan kin saukan Mugabe daga Mulki cikin salama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.