Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Jam'iyyar Mugabe na Zimbabwe na shirin tsige shi a yau

Shugaba Robert Mugabe tare da matarsa Grace Mugabe a wani taron Jam'iyyar ZANU-PF a cikin watan Oktoban da ya gabata
Shugaba Robert Mugabe tare da matarsa Grace Mugabe a wani taron Jam'iyyar ZANU-PF a cikin watan Oktoban da ya gabata REUTERS/Philimon Bulawayo

A yayin da Jam'iyyar ZANU-PF mai mulki a Zimbabwe ke shirin tsige shugaba Robert Mugabe a Majalisar Dokokin kasar a yau Talata, mataimakin shugaban da aka kora daga mukaminsa, Emmerson Mnangagwa ya bukaci Mugabe da ya gaggauta sauka daga kujerar mulkin kasar.

Talla

Sojojin kasar sun karbe ragamar tafiyar da mulkin kasar ne bayan Mugabe ya kori Mnangagwa a makon jiya, lamarin da ake kallo a matsayin yunkurin share fage ga  matarsa Grace Mugabe don gadon kujerar mulkin kasar.

Mr. Mnangagwa ya ce, ya tsere zuwa kasar waje ne makwanni biyu da suka gabata bayan ya samu bayanan da ke nuna cewa, ana kulla makircin kashe shi kuma ya ce, ba zai koma kasar ba har sai ya samu tabbaci game da tsaron lafiyarsa da rayuwarsa.

A wata zantawa da ya yi a sirce a wannan Talata, Mnangagwa ya ce, ya kamata Mugabe mai shekaru 93 ya mutunta kiraye-kirayen da ake yi ma sa na sauka daga kujerarsa wadda ya shafe shekaru 37 a kanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.