Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Robert Mugabe ya yi Murabus

Daruruwan 'yan kasar Zimbabwe, yayin da suke murnar saukar Robert Mugabe, daga shugabancin kasar. 21 ga Nuwamba, 2017.
Daruruwan 'yan kasar Zimbabwe, yayin da suke murnar saukar Robert Mugabe, daga shugabancin kasar. 21 ga Nuwamba, 2017. REUTERS/Mike Hutchings

Dubban ‘yan kasar Zimbabwe sun barke da bukukuwan murna, bayan samun tabbacin cewa shugaban kasar Robert Mugabe ya yi murabus.

Talla

Kakakin majalisar kasar Jacob Mudenda ne ya bada tabbacin murabus din na Mugabe, a cikin wasika da ya aikewa majalisar kasar a yau Talata, yayinda suke tsaka da muhawara, kan aiwatar da kudirin tsige shi.

Da fari daruruwan mutane sun yi dandazo a wajen ginin majalisar kasar ta Zimbabwe, inda suke zanga-zangar neman tilas, Robert Mugabe ya sauka daga shugabancin kasar.

Mafi akasarin ‘yan kasar ta Zimbabwe, musamman ‘yan adawa suna zargin Robert Mugabe da lalata tattalin arziki, tsarin dimokaradiya da kuma sashin shari’ar kasar, bayan shafe shekaru akalla 37 yana shugabanci.

'Yan dawar sun dora alhakin karyewar darajar kudin kasar da kuma hauhawar farashin kayan masarufi, bisa gazawar gwamnatin Mugabe.

Shekaru akalla 37, Mugabe ya shafe yana shugabancin kasar ta Zimbabwe, kafin karbe ragamar mulkin kasar da sojoji suka yi a makon da ya gabata, kwanaki kadan bayan da ya kori mataimakinsa Emmerson Mnangagwa daga mukaminsa, bisa zargin yana kokarin bijire masa.

Zalika Mugabe ya zargi Mnangagwa da kokarin haddasa rarrabuwar kai a jam’iyya mai mulki ta ZANU-PF.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.