Isa ga babban shafi
Kamaru

Kamaru ta bukaci mazauna kudu maso yammacin kasar su yi kaura

Ana farautar masu neman ballewa daga Kamaru
Ana farautar masu neman ballewa daga Kamaru STR / AFP

Hukumomin Kasar Kamaru sun bukaci dubban mutanen da ke kauyukan kudu maso Yammacin kasar da su bar gidajen su, yayin da aka girke sojoji domin farautar masu neman ballewa daga kasar da ke amfani da turancin Ingilishi.

Talla

Shugabannin Yankin Manyu sun bai wa mutanen kauyuka 16 umurnin barin gidajen su, inda suke cewa duk wanda ya zauna a gida za a dauke shi a matsayin mai taimakawa masu tada kayar baya.

Wani lauya mazaunin Yankin, Agbor Valery, ya ce tun a karshen mako ake girke sojoji dauke da manyan makamai a Yankin, yayin da mutane ke ci gaba da barin gidajen su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.