Isa ga babban shafi
Gabon

'Yan sandan Gabon sun kame mutane da dama a Libreville

Jami'an 'yan sandan gabon sun kai samame wata kasuwa a Libraville bayan harin da wani mai sai da nama ya kai wa 'yan kasar Denmark biyu.
Jami'an 'yan sandan gabon sun kai samame wata kasuwa a Libraville bayan harin da wani mai sai da nama ya kai wa 'yan kasar Denmark biyu. Getty Images

Jami’an ‘yan sanda a birnin Libreville na kasar Gabon, sun cafke mutane da dama mafi yawansu ‘yan asalin kasashen yammacin Afirika, bayan da wani da aka ce dan Nijar ne, ya daba wa wasu ma’aikatan talabijin na tashar National Geographic ‘yan kasar Danemark wuka.

Talla

Duk da cewa ba a bayyana sunan maharin ba, an bayyana cewa shekarunsu 59 ne kuma ya share akalla shekaru 19 zaune a kasar ta Gabon.

Mafi akasarin wadanda aka kame, bayan samamen da jami'an tsaron suka kai kan wata kasuwa a Libraville, Hausawa ne da suka shafe tsawon lokaci suna hada-hada.

A ranar Asabar mutumin ya kai wa wasu ‘yan kasar Denmark hari da wuka yana kabbara, sai dai rundunar 'yan sandan kasar ta zargi wadanda suka shaida kai harin da yunkurin hana sanar da ita halin da ake ciki, matakin da ta ce ta dauke shi a matsayin goyon baya ga aikata ta'addanci.

Rundunar ‘yan sandan Gabon ta ce, mutumin ya shaida mata cewa ya kai harin ne don maidawa Amurka Martani, bisa goyon bayan mai da birnin Kudus babban birnin kasar Isra’ila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.