Isa ga babban shafi

Majalisar Uganda ta soke dokar kayyade shekarun shugaban kasa

Zauren majalisar kasar Uganda, da ke babban birnin kasar Kampala.
Zauren majalisar kasar Uganda, da ke babban birnin kasar Kampala. REUTERS/James Akena

Majalisar Uganda ta kada kuri'ar amincewa da soke dokar da ta kayyade iyakacin shekarun da zasu ba da damar neman kujerar shugabancin kasar.

Talla

Matakin da zai bai wa shugaba Yoweri Museveni damar takarar wa’adi na 6 a shekarar 2021.

'Yan Majalisu 315 suka goyi bayan dokar, yayinda 62 suka ki amincewa da ita, sai kuma wasu 'yan majalisar guda biyu suka ki kada kuri’a kan kudurin.

Sabuwar dokar ta kawar da haramcin cewa duk mai shekaru 75 ba zai iya tsayawa takara ba, wanda ke nuna cewar shugaba Museveni wanda zai cika shekaru 77 lokacin zaben, zai iya sake neman zarcewa.

Kungiyoyin fararen hula sun yi watsi da matakin 'yan majalisar, wadanda suka sha alwashin kalubalantar dokar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.