Isa ga babban shafi
Uganda

Sojin Uganda da Congo sun kai farmakin hadin gwiwa kan 'yan tawaye

Dakarun kasar Uganda.
Dakarun kasar Uganda. ISAAC KASAMANI | AFP

Rundunar Sojin Uganda, ta kai Farmaki kan sansanonin ‘yan tawaye a gabashin kasar Congo, inda suke zargin maboya ce ga mayakan ‘yan tawayen kasar, da ake zargi da hallaka dakarun wanzar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya 14.

Talla

Sojin Ugandan sun kai farmakin ne da hadin gwiwar takwarorinsu na Congo, inda suka yi amfani da manyan makamai masu cin dogon zango, wadanda suka harba da cikin kasar ta Uganda.

Karo na farko kenan da kasashen na Uganda da Congo, suka hada gwiwa wajen kai wa mayakan ‘yan tawayen ADF farmaki.

Kakakin sojin Uganda Richard Karemire, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, farmakin ya biyo bayan musayar bayanan sirri tsakaninsu da takwarorinsu na Jamhuriyar Congo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.