Isa ga babban shafi
Muhallinka Rayuwarka

Illar magungunan feshi ga kasar Noma, Muhalli da lafiyar dan'adam

Sauti 20:00
Manoma na fuskantar kalubale dangane da amfani da magungunan kwari.
Manoma na fuskantar kalubale dangane da amfani da magungunan kwari. Reuters

Shirin "Muhallinka Rayuwarka" na wannan makon yayi tattaki zuwa Jamhuriyar Nijar, inda yayi nazari ne kan matsalar amfani da magunan feshi, wadanda a wani lokacin suke zama cikas ga manoma saboda da tsadarsu sannan da illolin magungunan ga dan Adam wani lokacin ma da muhalli. Bayan sakin ragamar kasuwanci da janye tallafin gwamnati wajen samar da maganin kashe kwari ga manoma yasa magunguna kala kala sun bazu a kasuwa, da suka hada da masu kyau da marasa kyau, wadanda kai tsaye ko ta wasu hanyoyi, illolinsu ke shafar lafiyar manoma da muhalli ba tare da manoman sun sani ba.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.