Isa ga babban shafi
Faransa

Za mu iya ƙara yawan dakarunmu a yankin Sahel-Macron

Emmanuel Macron tare da Mahamadou Issoufou a Yamai.
Emmanuel Macron tare da Mahamadou Issoufou a Yamai. LUDOVIC MARIN / AFP

A ci gaba da ziyarar da shugaban ke yi a jamhuriyar Nijar, Macron ya ce dakarun Faransa za su mayar da hankali sosai kan yanayin tsaro a yankin na sahel, koda za a buƙaci hakan a nan gaba.

Talla

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce ƙasarsa a shirye take ta ƙarfafa dakarunta da ke taimaka wa sojoji masu yaƙi da ƙugiyoyin tayar da ƙayar baya na muslunci a yankin sahel, idan buƙatar hakan ta taso.

A cewar sa Faransa za ta iya inganta ƙarfin dakarun nata ne saboda muhimmancin yaƙin da ake yi da ta’addanci a yankin na Sahel.

Sojojin ƙasashen Mali, da Niger, da Burkin Faso, da Chadi, da kuma na Mauritania ne ke aiki tare da dakarun Faransa guda 4000 a yankin na Sahel tun daga shekarar 2013, domin yaƙi da ta’addanci a arewacin ƙasar Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.