Isa ga babban shafi

Sojin Uganda sun yi ikirarin kashe ‘yan tawaye 100 a DR Congo

Rundunar Sojin kasar Uganda ta ce ta hallaka yan tawaye DR Congo 100
Rundunar Sojin kasar Uganda ta ce ta hallaka yan tawaye DR Congo 100 ISAAC KASAMANI | AFP

Rundunar Sojin kasar Uganda ta ce dakarun ta sun hallaka 'yan tawayen kungiyar UPDF sama da 100 da ke Gabashin Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo bayan kashe dakarun Majalisar Dinkin Duniya a makwannin da suka gabata.

Talla

Janar Richard Karemire, mai Magana da yawun ma’aikatar tsaron Uganda, ya ce bayan wadanda aka kashe an kuma jikkata wasu da dama.

Janar Karemire ya ce sun kaddamar da harin sama da kasa ne kan 'yan tawayen Allied Democratic Forces a sansanonin su guda 8 a wani hadin guiwar da suka yi da sojojin Congo.

Mai Magana da yawun sojin ya ce basu girke dakarun su a cikin kasar Congo ba, kuma babu wanda yaji rauni a harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.