Isa ga babban shafi
Kamaru

Kungiyar lauyoyin Afrika ta bukaci sakin shugabannin 'yan awaren Kamaru

Daruruwan al'ummar yankin da ke amfani da yaren Ingilishi na kasar Kamaru kenan, ke wata zanga-zangar nuna adawa da matakin wariyar da gwamnatin kasar ke nuna musu.
Daruruwan al'ummar yankin da ke amfani da yaren Ingilishi na kasar Kamaru kenan, ke wata zanga-zangar nuna adawa da matakin wariyar da gwamnatin kasar ke nuna musu. postnewsline

Kungiyar lauyoyin Afirka ta bukaci gwamnatin Najeriya da saki shugabannin masu fafutukar ballewar yankunan da ke amfani da turancin Ingilishi a Kamaru da aka cafke a birnin Abuja tun cikin makon jiya.

Talla

Duk da cewa gwamnatin Najeriya ta musanta bayanan da ke cewa an cafke wadannan mutane, to amma Hannibal Uwaifo, shugaban kungiyar lauyoyin na Afrika reshen Najeriya, ya ce tabbas an kama mutanen.

A cewar Hannibal Uwaifo bayan da suka samu tabbatacin cewa Najeriyar na rike da mutanen bayan cafke su a wani hotel da ke babban birnin kasar Abuja sun aikewa da ministan shara’a na Najeriyar wasika don samun karin bayani daga gare shi dama dalilan da suka sanya kama mutanen.

Mr Uwaifo ya ce Najeriyar ba ta da hujjar kama mutum ba tare da sammaci ba, na biyu ba wanda ya san dalilin kama wadannan mutane balantana sanin inda ake tsare da su, Inda ya bayyana kamen a matsayin wanda ya sabawa ka'ida.

Wasikar ta bukaci Najeriya ta sanar da duniya dalilin kama wadannan mutane daga nan kuma sai ta gaggauta bayar da umurnin sakinsu.

A cewarsa duk wani yunkuri na tasa keyarsu zuwa Kamaru, to hakan zai kasance sabawa dokokin kasa da kasa da ma dokokin Najeriya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.