Isa ga babban shafi
Somalia

Al-Shabab na tilastawa iyaye mika 'ya'yansu gareta

Tun a farkon shekarar 2015 ne kungiyar ta bude manyan makarantun addini a sassan kasar ta yadda ta ke yaye dalibi kan doron akidarta.
Tun a farkon shekarar 2015 ne kungiyar ta bude manyan makarantun addini a sassan kasar ta yadda ta ke yaye dalibi kan doron akidarta. (Photo : AFP)

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Right Watch ta ce kungiyar Al-Shabab da ke Somalia na tilastawa iyaye mika ‘ya’yansu gareta ta hanyar yi musu barazanar kai hare-hare yankunansu. Wani binciken kungiyar ya nuna cewa yanzu haka kungiyar ta tattara daruruwan kananan yara da ta kwato daga hannun iyayensu inda ta ke basu horo na musamman don zamowa mayakanta.

Talla

Rahoton da kungiyar ta fitar a jiya ya nuna cewa daruruwan yara ne a kasar ta Somalia da shekarunsu basu wuce 8 da haihuwa ba, ke gujewa yankunansu da makarantunsu don kaucewa fadawa hannun mayakan na Al-Shabab tun bayan fito da sabon salon na Alshabab cikin watan Satumban 2017 don kara yawan mayakanta.

Human Rights Watch ta kuma bayyana cewa awasu lokutan mayakan na Alshabab kan yi garkuwa da shugabannin yanki ko na addini tare da barazar hallaka su matukar iyaye basu amince da mika yaransu ga kungiyar ba.

Tun a farkon shekarar 2015 ne kungiyar ta bude manyan makarantun addini a sassan kasar ta yadda ta ke yaye dalibi kan doron akidarta.

Kungiyar ta ruwaito yadda shugaban wani kauye a yanki Bay da ke karkashin ikon Al-Shabab ya tabbatar da mika tarin kannana yara da shekarunsu ya fara daga 9 zuwa 15 bayanda suka yi alkawarin maido dasu bayan ‘yan kwanaki, sai dai bayan cikar kwanakin iyaye da dama da suka bukaci dawowar yaran nasu, kungiyar ta yi musu barazanar kisa.

Rahoton ya ce ko cikin watan Satumba, Al-shabab ta kwashe fiye da kananna yara 50 daga wasu makarantu biyu a yankin Burhakaba bayan da suka yiwa malaminsu jina-jina lokacin da ya yi tirjiyar mika yaran, haka zalika suka zane wani kankanin yaro dan shekaru 7 da ya nemi guduwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.