Isa ga babban shafi
africa ta kudu

Jam'iyyar ANC na shirin tsige Jacob Zuma

Shugaba Jacob Zuma na ci gaba da fuskantar kalubale baya ga zarge-zargen cin hanci da rashawa duk da cewa yana ci gaba da musantawa.
Shugaba Jacob Zuma na ci gaba da fuskantar kalubale baya ga zarge-zargen cin hanci da rashawa duk da cewa yana ci gaba da musantawa. REUTERS/Siphiwe Sibeko

Jam’iyya mai mulki ta ANC a Afrika ta kudu ta musanta batun shirye-shiryen tsige shugaba Jacob Zuma daga karagal Mulki kafin cikar wa’adinsa, da nufin shirye-shiryen tunkarar babban zaben kasar a shekara mai zuwa.

Talla

Wasu rahotanni da gidan talabijin na e-NCA a kasar ya ruwaito, ya ce kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na shirye-shiryen mikawa Jacob Zuma bukatar sauka daga mulki idan kuma ya ki shugancin jam’iyyar zai tsige shi da karfin tsiya.

Duk da cewar gidan talabijin ya boye sunan wanda ya bayar da bahasin amma kuma wani shafin labarai na Internate News24 ya ruwaito wani jigo a jam’iyyar da ya nemi a sakaya sunan na tabbatar da batun a safiyar yau Asabar.

Sai a shekarar 2019 ne wa’adin Jacob Zuma zagaye na biyu zai kammala, yayinda a bangare guda yak e ta cin karo da kalubale baya ga zarge-zargen cin hanci matakin da ya kai ga har aka kada masa kuri’ar yankan kauna.

Koda yake dai sabon shugaban kamitin gudanarwa na Jam’iyyar bai ce uffan kan batun ba, bayan wasu jerin taruka da suka gudanar karon farko tare da sabon shugaban jam’iyyar Cyril Ramaphosa a ranakun Alhamis da Juma’a.

Shima dai mai Magana da yawun jam’iyyar ta ANC, yayin tattaunawarsa da manema labarai ya ce baya da hurumin yin karin haske kan batun har sai zuwa lokacin da kwamitin ya kammala tattaunawa.

Babban sakataren jam’iyyar Ace Magashule ya ce batun tsige Zuma ba ya cikin jerin batutuwan da suke tattaunawa yayin babban taron da yanzu haka su ke ci gaba da gudanarwa.

Ana dai kyautata zaton Cyril Ramaphosa wanda yam aye gurbin Zuma a matsayin shugaban jam’iyya na kuma shirye-shiryen maye gurbinsa a matsayin shugaban kasa, la’akari da yadda a baya-bayan nan ya ke ci gaba da bankado badakalar cin hanci kan shugaban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.