Isa ga babban shafi
Buhari

Buhari ya gana da Obasanjo a cikin raha

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, tare da tsaffin shugabannin Najeriya, Olusegun Obasanjo da kuma Janar AbduSalam Abubakar, yayin da suke halartar taron kungiyar tarayyar Afrika AU da ke gudana a birnin Addis Ababa na kasar Habasha.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, tare da tsaffin shugabannin Najeriya, Olusegun Obasanjo da kuma Janar AbduSalam Abubakar, yayin da suke halartar taron kungiyar tarayyar Afrika AU da ke gudana a birnin Addis Ababa na kasar Habasha. Femi Adesina/Facebook

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo, a babban birnin kasar Habasha, Addis Ababa, inda ake taron shugabannin nahiyar Afrika.

Talla

Shugabannin biyu sun gaisa cikin raha, inda suka yi wata gajeriyar ganawa, kafin daga bisani shi ma tsohon shugaban Najeriya Janar AbduSalam Abubakar ya iso wajen shugabannin inda suka dauki hotuna.

Haduwar shugabannin ta zo mako guda bayan da tsohon shugaba Obasanjo, ya rubuta budaddiyar wasika ga Muhammadu Buhari inda ya shawarce shi da kauracewa sake neman shugabancin Najeriya karo na biyu a 2019.

Cikin wasikar, tsohon shugaban ya zargi Buhari da gazawa wajen farfado da tattalin arzikin Najeriya, kawar da idanu kan aikata ba dai dai ba da wasu makusanta ke yi, da kuma sauran zarge zarge.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.