Isa ga babban shafi
Afirka

Cutar da ke gab da kunno kai Afirka

Akwai kasashe da dama da ke cikin hadarin fama da yunwa a Afirka.
Akwai kasashe da dama da ke cikin hadarin fama da yunwa a Afirka. RFI / Gaël Grilhot

Yawancin mutane a Afirka sun rungumi cin kayan makulace hannu bibbiyu, musamman waɗanda ake shigowa da su daga ƙasashen waje, tare da yin watsi da wasu ɗabi'u na motsa jiki, abinda da ke saka su cikin haɗarin fama da ƙibar da ta zarce misali.

Talla

A Burkina-Faso da ke kudancin Afirka, yawan masu fama da ƙiba ya lunka sau 1,400 a cikin shekaru 34, yayin da a Ghana, da Togo, da Ethiopia da kuma Benin ya lunka sau 500- In ji cibiyar ƙididdiga kan harkar lafiya ta jami'ar Washington.

Yanzu haka akwai wadatar ababen hawa irin su motoci da babura, wanda hakan ya rage ɗabi'ar takawa da ƙafa a tsakanin al'umma, kuma da dama daga cikin su sun watsar da noma, inda suke komawa cikin birane.

Masana lafiya sun ce yaran da suka taso ba tare da isassun sinadaren da jiki ke bukata ba, sun fi faɗawa cikin haɗarin fama da ƙibar da ta wuce misali lokacin da suka samu wadatar abinci.

A cewar jaridar New York Times, ƙiba, za ta iya zama cuta mai wahalar magancewa tsakanin al'ummar Afirka saboda dalilai da dama.

Daga cikin dalilan kuwa su ne: an fi mayar da hankali a ɓangaren magance cututtuka irin su HIV/AIDS, da zazzabin cizon sauro, da kuma tarin-fuka, waɗanda ake gani a matsayin manyan cututtuka, yayin da ba a mayar da hankali wajen magance cututtuka irin su hawan jini da ciwon zuciya ba.

Sai dai, duk da cewa ƙiba na kara yawaita a Afirka, da alama har yanzu ba a daina fama da yunwa ba.

Ko a watan Maris na bara, Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa bala'in yunwa zai iya ɓarkewa a ƙasashe irin su Somalia, da Najeriya, da Sudan ta kudu saboda rikice-rikice-In ji jaridar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.