Isa ga babban shafi
Najeriya

Patience Jonathan na son tattaunawa da EFCC a wajen kotu

Uwargidan tsohon shugaban Najeriyar Patience Jonathan ta bakin lauyan ta bukaci tattauna da hukumar ta EFCC don kawo karshen shari'un da ta ke fuskanta kan boye wasu makudan kudade.
Uwargidan tsohon shugaban Najeriyar Patience Jonathan ta bakin lauyan ta bukaci tattauna da hukumar ta EFCC don kawo karshen shari'un da ta ke fuskanta kan boye wasu makudan kudade. NAN

Uwargidan Tsohon shugaban Najeriya, Patience Jonathan ta rubutawa Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar wato EFCC wasika, inda ta ke bukatar yin sulhu domin kawo karshen tuhumar da ake mata na mallakar wasu makudan kudade ta hanyar da basu kamata ba.

Talla

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ya ruwaito cewar, lauyar matar tsohon shugaban, Ifedayo Adedipe, ya rubuta wasikar a madadin wanda ya ke karewa, inda ya bukaci EFCC ta sanya wata rana da bangarorin za su zauna domin kulla yarjejeniya.

Wasikar ta ce, a matsayin Adedipe na lauyar Patience Jonathan, da kuma kamfanonin da ke alaka da ita da kungiyoyi, sun amince su tinkari hukumar domin tattaunawa kan daukacin kararrakin da EFCC ta shigar domin warware su a wajen kotu.

Lauyan ya ce, suna da yakini kulla yarjejeniya a wajen kotun, zai taimakawa bangarorin biyu.

Kamfanin dillancin labaran Najeriyar, ya ce wasikar ta Patience Jonathan na zuwa ne a daidai lokacin da EFCC ta gano wasu karin asusun ajiya guda biyu a bankunan Skye Bank da First Bank dauke da makudan kudade mallakar matar tsohon shugaban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.