Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Jacob Zuma ya yi murabus

Shugaban Afrika ta Kudu mai murabus, Jacob Zuma.
Shugaban Afrika ta Kudu mai murabus, Jacob Zuma. REUTERS / Siphiwe Sibeko

Kasar Afirka ta kudu ta kama hanyar samun sabon shugaban kasa yau, sakamakon murabus din shugaba Jacob Zuma daren jiya.

Talla

Shugaban Jam’iyyar ANC, kuma mataimakin Zuma, Cyrila Ramaphosa, shi ne zai maye gurbin sa a matsayin shugaban kasa.

Bayan an dauki dogon lokaci ana dambarwar siyasa, da barazanar tsige shugaba Zuma, daren jiya shugaban ya yi wa al’ummar kasar jawabi, inda ya bayyana saukar sa cikin gaggawa.

Yayin jawabin nasa Zuma, ya ce babu hujjar da zata sa wani ya rasa ransa a dalilin goyon bayan da ayke bashi, zalika ba zai bari a samu rarrabuwar kawuna a Jam’iyyar ANC ba, domin haka ne ya yanke hukuncin sauka daga mukamin shugaban Afrika ta Kudu a matsayinsa na dan Jam’iyya mai ladabi da biyayya.

Wani lokaci a yau Alhamis ko gobe Juma’a ake sa ran, majalisar kasar ta kada kuri’ar amincewa da zabar Cyril Ramaphosa a matsayin sabon shugaban kasar Afrika ta Kudu, wanda aka zaba a matsayin shugaban jam’iyyar ANC mai mulki, a watan Disambar bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.