Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Anyi jana’izar shugaban 'Yan adawar Zimbabwe, Morgan Tsvangirai

Dubban mutane na juyayin faretin karshe da akayi wa Morgan Tsvangirai a Harare, Zimbabwe 19 ga watan Fabarerun 2018
Dubban mutane na juyayin faretin karshe da akayi wa Morgan Tsvangirai a Harare, Zimbabwe 19 ga watan Fabarerun 2018 REUTERS/Philimon Bulawayo

Dubban Mutane ne suka halarci jana’izar shugaban Yan adawar kasar Zimbabwe, Morgan Tsvangirai, daya daga cikin yan siyasar Afirka da ya samu karbuwa a kasashen duniya, kuma an gudanar da jana'izar a kauyen su dake Buhera.

Talla

Shidai marigayin da ya yi fice wajen kalubalantar mulkin shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe, ya rasu ne ranar laraba da ta gabata, yana da shekaru 65, sakamakon cutar kansar da ya yi fama da ita a wani asibiti dake kasar Afirka ta kudu.

An dauki gawar sa daga birnin Harare a wani jirgin saman soji zuwa kauyen su dake Buhera, mai nisan kilomita 220 daga Harere, tare da rakiyar mahaifiyar sa Mbuya Tsvangirai.

Dubban mutane suka halarci jana’izar, wasu sanye da jajayen kayar dake nuna alamar jam’iyyar sa, kana da usur da suka yi ta busawa, yayin da wasu suka yi ta zub da hawaye.

Cikin wadanda suka halarci jana’izar harda shugaban Yan adawar Kenya, Raila Odinga, wanda ya soki shugabannin Afirka kan yadda suke murkushe yan adawa.

Odinga yace kowa ya san Tsvangirai ya kada Mugabe a zagayen farko na zaben shekarar 2008 amma aka murde masa, abinda ya haifar da tashin hankalin da aka kafa gwamnatin hadin kan da aka bashi Firaminista.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.