Isa ga babban shafi
Burkina Faso,Faransa

Shuwagabanin Addini a Burkina Faso sun bukaci al'ummar kasar da su hada kai su tunkari Yan ta'adda

jihadistes au sahel
jihadistes au sahel france24

Shuwagabanin addinin musulunci da na kirista a Burkina faso sun yi tir da harin ta’addancin Wagadugu, kan shelkwatar tsaron kasar da kuma ofishin jakadancin Faransa dake birnin.

Talla

A cikin wata sanarwa a yau shugaban hadaddiyar kungiayar addainin musulnci ta Burkina Faso (FAIB) a takaice, Cheick Abubakar Maiga na 2, Ya bayyana harin ta’addancin na ranar juma’ar da ta gabata da zama rashin imani, kuma marar hujja a tsarin musulunci.

Bugu da kari Cheick Abubakar Maiga na 2, ya yi kiran dukanin ‘yan kasar ta Burkina Faso maza da mata da su hada kai su yaki makiya, dake haddasa masu zaman zullumi.

A nasa bangaren shugaban mabiya mazahabar katolika na birnin Wagadugu kardinal Philippe Ouedraogo yayi tir da harin, inda ya bayyana cewa daga nasu bangaren kristoci, Kalachnikov dinsu ta mayar da martini, ita ce addu’ar Allah ya baiwa kasar zaman lafiya

shidai wannan hari da ya girgiza kasar Burkina Faso irinsa na uku da aka kai a kasar, kasa da shekaru biyu, wata kungiyar dake ikrarin jihadi ce ta dau nauyin kaishi, a matsayin ramuwar gayya kan kisan daya daga cikin baradanta Hassan al-Ansari da dakarun Faransa suka yi a kasar Mali.

Wayen ma Hassan al-Ansari, wanda sunansa na gaskiya, Mohamed Ould Nouini, dan asalin yankin arawacin Mali ne.

A karo na farko yafara bayyana ne, a cikin wani hoto da aka dauka a cikin watan maris din 2017 a lokacin da suka bayyan kafa kungiyar gwagwarmaya da makamai dake ikrarin taimakawa musulunci da musulmi a duniya (GSIM) tun a wannan lokaci ne ya zama wakilin kungiyar a yankin Gao dake arwacin Mali.

Hassan al-Ansari dai, ya taba zama shugaban dakarun kungiyar Al-Murabitun, tsohuwar kungiyar da dan kasar Aljeriyar nan, Belkmokhtar ya kafa. Bayan da yam aye gurbin wani jigon a kungiyar ya fadi cewa da Ahmed al-Tilemsi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.