Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Jacob Zuma zai gurfana gaban kotu kan Rashawa

Cikin tuhume tuhumen da za’a yiwa tsohon shugaban sun hada da cin hanci da rashawa da halarta kudaden haramun da kuma almundahana.
Cikin tuhume tuhumen da za’a yiwa tsohon shugaban sun hada da cin hanci da rashawa da halarta kudaden haramun da kuma almundahana. REUTERS / Siphiwe Sibeko

Mai Gabatar da kara a kasar Afirka ta kudu ya ce za’a gurfanar da tsohon shugaban kasar Jacob Zuma a gaban kotu, domin tuhumar sa da laifufukan da suka shafi cin hanci da rashawa lokacin da yake rike da shugabancin kasar.

Talla

Shaun Abrahams, Daraktan gabatar da kararraki na kasar, ya ce bayan nazari kan zargin da ake yiwa tsohon shugaban kasar, ya yanke hukuncin cewar za’a samu nasarar tuhumar tsohon shugaban.

Cikin tuhume tuhumen da za’a yiwa tsohon shugaban sun hada da cin hanci da rashawa da halarta kudaden haramun da kuma almundahana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.