Isa ga babban shafi
Najeriya

Shugaba Buhari ya janye daga taron kasashen Afrika na Kigali

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari REUTERS/Dan Kitwood

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya janye daga taron kungiyar kasashen Afirka da aka shirya gudanarwa ranar laraba a Kigali, domin rattaba hannu kan yarjejeniyar kasuwancin bai daya tsakanin kasashe 54 dake nahiyar.

Talla

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, Tope Elias-Fatile ya ce shugaban ya janye ne domin bada damar ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan harkokin kasuwanci.

Kungiyar kwadagon Najeriya ta bayyana rashin amincewar ta da shiga yarjejeniyar wadda ta ce zata tilastawa masana’antu rage ma’aikata

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.