Isa ga babban shafi
Afrika

Morocco na fatan samun amincewar Fifa wajen shirya gasar shekarar 2026

Tambarin hukumar kwallon kafa na Duniya Fifa
Tambarin hukumar kwallon kafa na Duniya Fifa REUTERS/Arnd Wiegmann/Files

Hukumomin Moroco a karshen makon da ya gabata sun gabatar da sunayen wasu birane 12 tareda wasu filayen wasanni 14 zuwa hukumar kwallon kafa ta Duniya Fifa a kokarin su na samu amincewar hukumar domin karbar bakucin gasar cin kofin Duniya na shekara ta 2026.

Talla

Shugaban kwamity dake shugabantar tawagar Morocco a wannan tafiya Moulay Hafid Elalamy a wata ganawa da manema labaran Duniya a birnin Casablanca ya bayyana cewa suna da hurumin gani kasar da sunan nahiyar Afrika ta samu amincewar hukumar Fifa domin karbar bakucin wasannin na shekarar ta 2026.

Hafid Elalamy ya bayyana damuwa musaman ganin ta yada aka samu hadin guiwar kasashen Amurka,Canada da Mexico da suka bukaci Fifa ta amince da su don ganin sun dau nauyin karbar bakuncin gasar cin kofin Duniya na shekarar ta 2026.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.