Isa ga babban shafi
Senegal

Kotun Senegal ta daure Sall shekaru biyar a gidan yari

Khalifa Sall da kotun Senegal ta daure shekaru biyar a gidan yari saboda almundahana
Khalifa Sall da kotun Senegal ta daure shekaru biyar a gidan yari saboda almundahana SEYLLOU / AFP

Wata kotu a Senegal ta yanke wa daya daga cikin fitatun 'yan siyasar kasar, Khalifa Sall hukuncin daurin shekaru biyar a gidan yari saboda samun sa da laifin almundahana. Masu sa ido a siyasar kasar na kallon matakin a matsayin wani yunkuri na hana shi kalubalantar shugaba Macky Sall a zaben shekarar 2019.

Talla

Kotun ta ce, ta samu Khalifa Sall wanda ya rike mukamin Magajin Garin Birnin Dakar da laifin amfani da kudaden gwamnati ta hanyar da ba ta kamata ba, abin da ya sa aka daure shi shekaru 5 a gidan yari da kuma cin tarar sa Cefa miliyan 5 ko kuma Euro dubu 7da 625.

Kotun ta ce, ta gamsu da shaidun da aka gabatar ma ta wadanda suka hada da cin amana da halarta kudaden haramun da kuma ruf da ciki da kudaden talakawa.

Masu gabatar da kara sun bukaci a daure Sall shekaru 7 a gidan yari da kuma cin sa tarar Dala miliyan 10, amma sai alkalin kotun ya amince da daurin shekaru 5.

Lauyan dan siyasar, Cheikh Khouraissi Ba ya ce, zai daukaka kara domin kalubalanatar hukuncin a shari’ar da ta dauke al’ummar kasar hankali saboda farin jinin da dan siyasar ke da shi.

Magoya bayan Sall da suka cika kotun sun yi ta bayyana rashin amincewarsu da hukuncin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.