Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Jacob Zuma gaban alkalan kotu a Durban

Jacob Zuma tsohon Shugaban kasar Afrika ta Kudu
Jacob Zuma tsohon Shugaban kasar Afrika ta Kudu REUTERS/Sumaya Hisham/File Photo

Dubban magoya bayan tsohon shugaban kasar Afirka kudu Jacob Zuma ne ake saran yau juma’a za su gudanar da zanga zanga zuwa kotun Durban, inda ake saran gurfanar da shi kan zargin cin hanci da rashawa.

Talla

Shari’ar tsohon Shugaban kasar za ta gudana ne a yankin Kwa-Zulu Natal, hakan zai kasance daya daga cikin zakaran gwajin dafi, ganin yadda shugabanin Afirka ke kaucewa tuhuma duk da tabargazar da suka yi, lokacin da suke rike da madafan iko.

Kungiyoyin addini da magoya bayan Zuma sun kwashe daren jiya suna zaman dirshe, inda suke bayyana cewar ana amfani da siyasa ce domin musgunawa gwarzon na su.

Mai Gabatar da kara a kasar Afirka ta kudu Shaun Abrahams ya ce za’a gurfanar da tsohon shugaban kasar Jacob Zuma a gaban kotu, domin tuhumar sa da laifufukan da suka shafi cin hanci da rashawa lokacin da yake rike da shugabancin kasar tareda rike .

Shaun Abrahams, daraktan gabatar da kararraki na kasar, ya ce bayan nazari kan zargin da ake yiwa tsohon shugaban kasar, ya yanke hukuncin cewar za’a samu nasarar tuhumar tsohon shugaban.

Zuma ya isa da safiyar yau kotun dake Durban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.