Isa ga babban shafi
Kamaru

'Yan awaren Kamaru sun yi garkuwa da wani babban Alkali

Wasu Tarin Jami'an tsaro kenan da gwamnatin Kamaru ta girke a yankin da ke amfani da turancin Ingilishi inda ake fama da rikici.
Wasu Tarin Jami'an tsaro kenan da gwamnatin Kamaru ta girke a yankin da ke amfani da turancin Ingilishi inda ake fama da rikici. AFP

Wasu 'yan bindiga a yankin 'yan awaren kasar Kamaru masu amfani da yaren Ingilishi sun sace daya daga cikin manyan tsoffin alkalan kasar Mai shari'a Martin Mbeng.

Talla

A bara ne Mai shari'a Martin Mbeng ya yi ritaya a matsayin mataimakin shugaban alkalan kotun koli a kudu maso Yammacin kasar da ke makotaka da Arewa maso yammaci inda tashin hankali ya yi kamari.

Lauyan kuma abokin sa Agbor Nkongho ya ce Mbeng na hannu masu neman ballewa daga kasar, Bayan sun kama shi jiya da safe.

Nkongho ya yi watsi da garkuwa da tsohon alkalin, inda ya bukaci gaggauta sakin sa.

A baya-bayan nan dai tashe-tashen hankula masu alaka da satar mutane kisan ba gaira babu dalili da kuma karancin tsaro na ci gaba da tsananta a yankin mai amfani da turancin Ingilishi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.