Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Mugabe zai gurfana gaban Majalisar kasar kan bacewar dala biliyan 15

Majalisar ta ce dole ne Mugabe ya gurfana gabanta don yin jawabi kan bacewar kudin la'akari da cewa a lokacin mulkinsa ne suka bace.
Majalisar ta ce dole ne Mugabe ya gurfana gabanta don yin jawabi kan bacewar kudin la'akari da cewa a lokacin mulkinsa ne suka bace. Phill Magakoe / AFP

Kwamitin da Majalisar kasar Zimbabwe ta kafa domin gudanar da bincike kan zargin asarar da kasar ta tafka wajen cinikin lu’u lu’u ya sha alwashin gayyatar tsohon shugaban kasar Robert Mugabe don bada shaida a gaban ta.

Talla

Majalisar ta ce za ta bukaci Mugabe ya yi musu bayani kan bacewar Dala biliyan 15 a shekarar 2016 daga kudaden shigar da ake samu wajen hakar ma’adinin saboda cin hanci da kuma kaucewa biyan haraji.

Temba Mliswa, shugaban kwamitin binciken ya ce suna bukatar Mugabe ne a matsayinsa na wanda ya ke kan karagal mulki lokacin bacewar kudin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.