Isa ga babban shafi
Kamaru

'Yan wasan Kamaru sun yi batan dabo a Australia

Tuni dai aka baza jami'an tsaro akan iyakokin kasar don lalubo inda 'yan wasan suka shiga.
Tuni dai aka baza jami'an tsaro akan iyakokin kasar don lalubo inda 'yan wasan suka shiga. REUTERS

Akalla 'yan wasan kasar Kamaru da ke halartar gasar wasannin kasashe renon Ingila 8 ne suka bata a kasar Australia, matakin da ya jefa masu kula da su cikin rudani.Bayanai na nuna cewa, 'yan wasan sun fito ne daga Yankin da ake amfani da Turancin Ingilishi mai fama da tashin hankali.

Talla

Jami’in yada labaran tawagar 'yan wasan Kamaru da ke halartar gasar wasannin, Simon Molombe, ya tabbatar da bacewar Yan wasan, wadanda suka hada da masu daga nauyi guda 3 da Yan dambe guda 3.

Molombe ya ce tuni aka shaidawa 'yan Sandan Australia domin gudanar da bincike kan lamarin wanda suka bayyana shi a matsayin abin takaici.

Manajan da ke kula da 'yan wasan Victor Agbor Nso ya ce sun yiwa Yan Sanda bayani kan lamarin domin ganin an gano inda 'yan wasan suka shiga.

Kafin dai fara wasannin, Ministan cikin gidan Australia Peter Dutton ya gargadi 'yan wasan cewar za’a sa ido akan su sosai domin ganin duk abinda su ke aikatawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.