Isa ga babban shafi
Najeriya

Sabuwar jam'iyyar siyasa a Najeriya

Olusegun Obasanjo, tsohon Shugaban Najeriya
Olusegun Obasanjo, tsohon Shugaban Najeriya AFP PHOTO / SEYLLOU

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, ya ce kawancen CNM da ya ke jagoranta ya rikide zuwa jam’iyyar siyasa mai suna African Democratic Congress, ADC.

Talla

Obasanjo, wanda ya sanar da sunan sabuwar jam’iyyar, ya ce ba zai kasance mamba a cikinta, amma ko shakka babu manufofinta sun sha bamban da na PDP da kuma APC a cewarsa.

Tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo, ya ce ba zai taba goyan bayan aniyar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ta sake tsayawa takarar shugabancin kasar wa’adi na biyu ba.

Obasanjo ya kara da cewa dukkanin kalaman da ya furta akan shugaba Buhari cikin wasikarsa ta ranar 23 ga watan Janairun wannan shekara inda ya shawarce shi da janye aniyar tazarce suna nan daram, bai janye su ba.

Tsohon shugaban na Najeriya ya bayyana haka ne ta hannun mai bashi shawara akan kafafen yada labarai Kehinde Akinyemi, yayinda yake karyata rahotannin da ke cewa a halin yanzu ya janye adawar da yake wa shugaba Muhammadu Buhari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.