Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan majalisun Najeriya sun yi barazanar tsige Buhari

Zaman hadaka na majalisun tarayyar Najeriya wanda ke da nufin matsa kaimi ga shugaban kasar Muhammadu Buhari don ya amsa bukatunsu ko kuma su tsige shi.
Zaman hadaka na majalisun tarayyar Najeriya wanda ke da nufin matsa kaimi ga shugaban kasar Muhammadu Buhari don ya amsa bukatunsu ko kuma su tsige shi. venturesafrica

Majalisar Dokokin Najeriya da ta kunshi ta Dattawa da ta Wakilai sun yi barazanar amfani da karfin da kundin tsarin mulki ya basu wajen daukar mataki kan shugaban kasar Muhammadu Buhari muddin yaki amincewa da bukatunsu.

Talla

Bayan wani zaman hadin gwiwa na masamman da majalisun suka gudanar yau, Shugaban Majalisar Dattijai Bukola Saraki ya gabatar da bukatu 11 da su ke bukatar shuagabn kasar Muhammadu Buhari ya aiwatar ko kuma su dauki matakai akanshi.

Bukatun sun hada da bai wa shugabannin rundunonin tsaro umarnin kawo karshen kashe-kashen da ake samu a sassan kasar da kuma daina cin zarafin 'Yan Majalisu da bangaren zartaswa.

'Yan majalisun sun bukaci shugaba Buhari ya dauki alhakin duk ayyukan da wadanda ya nada suka yi tare da kada kuri'ar yankan kauna ga sufeto Janar na 'Yansandan kasar Ibrahim Idris.

'Yan majalisun sun kuma bukaci Buhari ya nuna gaskiya wajen yaki da cin hanci da rashawa sabanin yadda ya ke yi a yanzu.

Haka zalika 'yan majalisun sun ce za su gana da da hukumomin duniya da suka kunshi ECOWAS, kungiyar tarayyar Turai da kuma Majalisar Dinkin Duniya da nufin kare dimokradiyyar kasar wadda ke fuskantar barazana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.