Isa ga babban shafi
Kamaru

Amnesty ta ce Soji a Kamaru na zafafa rikici a yankin ‘yan a ware

Wani ginin da aka kona a kasar Kamaru a 2017
Wani ginin da aka kona a kasar Kamaru a 2017 REUTERS/Josiane Chemou

Kungiyar Kare hakkin Bil Adama ta Amnesty International ta ce yadda jami’an tsaron Kamaru ke dirar mikiya kan yan awaren da su ke a yankin da ake amfani da Turancin Ingilishi na dada zafafa rikici a Yankin.

Talla

Wani rahoto mai kumshe da shafuka 37 da kungiyar ta Amnesty International ta fitar, ya yi bayani kan kashe kashen da jami’an tsaro su ke yi ba tare da dalili ba, da lalata dukiyar jama’a da kuma kama mutane da azabtar da su tun daga karshen shekarar da ta gabata.

Rahotan yace amfani da karfin da ya wuce kima da jami’an tsaro keyi kan mutanen yankin ya haifar da samun matasan da suke daukar makamai domin kare kan su da kuma ci gaba da fafutuka.

Ya zuwa yanzu dai gwamnatin Kamaru bata mayar da martani kan rahotan ba, amma a baya an sha samun rahotanni daga kungiyoyin da ba na gwamnati ba, da daidaikun jama'a da kan bayyana yadda Sojin kasar ke gallaza wa mutane bisa zargin abinda ba su aikata.

Akwai ma hotunan bidiyo dasuka yadu a kafaifansadarwa na zamani a yanar Gizo inda ake nuna yadda Sojin ke yi wa mutane bugun kawo Wuka tare da azabtar da su ba tare da an gurfanar da su a gaban kuliya ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.