Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa na zargin Mali da kin zaman lafiya a yankin Sahel

Le G5 Sahel à Sévaré, au Mali, le 30 mai 2018.
Le G5 Sahel à Sévaré, au Mali, le 30 mai 2018. SEBASTIEN RIEUSSEC / AFP

Hukumomi a kasar Faransa sun zargi kasar Mali da yi wa shirin samar da zaman lafiya a yankin Sahel zagon-kasa ta hanyar kaucewa sakamakon yarjejeniyar.

Talla

A lokacin wata ganawar da ya yi da takwaransa a birnmin Stockholm na kasar Sweden a jiya, ministan harkokin wajen Faransa Jean Yves Le Drian ya zargi kasar Mali da rashin kudurin sasanta siyasar yankin Sahel ta hanyar kin yin aiki da yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma a yankin sahel

A lokacin ziyarar da ya kai a birnin Stockholm na kasar Sweden a jiya ministan harkokin wajen kasar ta Faransa ya bayyana cewar yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma ta birnin Alger ta kunshi duk wasu batutuwan da ya kamata a ce sun samar da zaman lafiya a kasar ta Mali

Abinda ya rage kawai shine a samar da niyar siyasa ta gari da za ta ba da damar sarrafa yarjejeniyar ta zama a aikace, abinda ya ce ba shi bane a halin yanzu ke wakana, wanda kuma ya ce yana fatan ganin hakan ya tabbata bayan zaben shugabancin kasar ta mali da za a yi nan da makwanni 2 masu zuwa

Yarjejeniyar zaman lafiyar birnin Alges na kasar Aljeriya da aka rattaba wa hannu a tsakanin gwamnatin Mali da ‘yan tawaye a 2015 karkashin jagorancin Majalisar dinkin Duniya, wadda ta tanadi kawo karshen mayakan jihadi a kasar ta Mali, har yanzu an gagara yin amfani da ita a wasu yankunan kasar ta Mali da ke karkashin ikon dakarun gwamnatin Mali, Faransa da kuma Majalisar dinkin Duniya.

Bisa wannan dalili ne in ji Jean Yves Le Drian yanzu haka tashe-tashen hankullan sun yadu a cikin kasashen BF da Jamhuriyar Nijar da ke makwabtaka da malin da a wani lokaci ke hadawa da rikice-rikice tsakanin alummomi

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.