Isa ga babban shafi

Shugaban Zimbabwe ya tsallake rijiya da baya

Shugaban kasar Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa.
Shugaban kasar Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa. Jekesai NJIKIZANA/AFP

Shugaban Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya ce ya tsira daga yunkurin da akai na hallaka shi, a wani harin bam da aka kai kan taron jam’iyyarsa ta Zanu-PF a yau Asabar, inda aka jikkata mataimakinsa Kemo Mohadi da sauran shugabannin jami’yya.

Talla

Mutane da dama ne suka jikkata bayan fashewar Bam din yayin taron yakin neman zaben da ya gudana a birnin Bulawayo na biyu mafi girma a kasar ta Zimbabwe inda ake gangamin zaben shugabancin kasar da aka shirya za a yi a karshen watan Yuli mai zuwa.

Har yanzu dai jami’an agaji ko bangaren gwamnati basu bayyana adadin wadanda suka jikkata a harin ba.

Zaben shugabancin Zimbabwe da za a yi a ranar 30 ga watan Yuli mai kamawa, shi ne na farko a kasar, tun bayan da tsohon shugaba mai murabus, wato Robert Mugabe ya dare shugabancin kasar a shekarar 1980.

Harin bam din dai ya zo ne sa’o’i kalilan, bayan da aka kai makamancinsa a birnin Addis Ababa, kan taron gangamin goyon bayan sabon Firaministan Habasha Abiy Ahmed, inda akalla mutane 83 suka jikkata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.