Isa ga babban shafi

Harin bam ba zai hana mu yin zaben shugaban kasa ba - Zimbabwe

Jami'an agaji, yayin da suke bai wa wadanda harin bam a taron yakin neman zaben jam'iyyar Zanu-PF a birnin Bulawayo, taimakon gaggawa.
Jami'an agaji, yayin da suke bai wa wadanda harin bam a taron yakin neman zaben jam'iyyar Zanu-PF a birnin Bulawayo, taimakon gaggawa. Tafadzwa Ufumeli/via REUTERS

Gwamnatin Zimbabwe ta ce, harin bam din da aka kai kan taron yakin neman zaben jam’iyya mai mulki,, ta Zanu-PF da shugaban kasar Emmerson Mnangagwa ke jagoranta, ba zai sa a dage zaben shugabancin kasar da aka shirya za a yi, a ranar 30 ga watan Yuli mai zuwa ba.

Talla

Kwana guda bayan kai harin da shugaba Mnangagwa ya ce shi aka son hallakawa, rundunar ‘yan sandan kasar ta ce mutane 49, suka jikkata a harin.

Daga cikin wadanda harin na birnin Bulawayo ya rutsa da su akwai mataimakan shugaban kasar guda biyu, wato, Kembo Mohadi da Constantino Chiwenga.

Zaben shugabancin kasar da za a yi nan da makwanni 5, shi ne na farko da zai gudana, tun bayan fara mulkin shugaba Robert Mugabe mai Murabus da ya shafe shekaru 37 yana jagorancin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.